Nijeriya : “Gaba kura baya sayaki” : Mmagance mummunan tasirin da rikicin arewa maso gabashin Nijeriya ke da shi a kan yara

Wannan rikici na Arewa maso gabashin Nijeriya ya yi mummunan tasiri ga yara. Boko Haram sun yawaita sace yara mata da maza sannan su sake jefa su cikin wasu ayyukan ta’asa; ta jefa al’ummomi cikin bala’i a faɗin yankin, ta hanyar hare-hare da wawashe (dukiyar) farar hula da makarantu. Maimakon kare yaran da ke kuɓutowa daga hannun Boko Haram, sai sojojin Nijeriya su tsare su na tsawon watanni ko shekaru ba bisa ƙa’ida ba kuma su azabtar da su da sauran hanyoyin gallazawa. Bayan haka rundunar sojin ta kasa samar wa yara ‘yan gudun hijira damar samun ilimi wadatacce.

Choose a language to view report

Download PDF