Nijeriya: “Ina cikin baƙin ciki” – Yanayin da tsofaffi suka tsinci kansu na tashin hankali da gudun hijira da kuma tsarewa a arewa maso gabashin Nijeriya

Rikicin arewa maso gabashin Nijeriya yana shekararsa ta ashirin ke nan a halin yanzu, inda ‘yan Boko Haram da sojojin Nijeriya suke da alhakin laifukan yaƙi da wasu laifukan take haƙƙin ɗan Adam. A cikin wannan yanayi ne kuma ake watsi da sha’anin tsofaffi, duk da cewa su ke faɗawa haɗari na musamman a ƙauyukansu da wajen tsarewar sojoji da gudun hijira. Rahoton ya duba ayyukan cin zarafi na musamman ga tsofaffi ciki har da inda tsufa da nakasa suka haɗu ga jinsin namiji ko mace. Har wa yau rahoton ya yi nazari a kan yadda aikin bayar da tallafi ya gaza kula da haƙƙoƙin tsoffi na ba su abinci da magunguna da matsuguni da rashin damawa da su.

Choose a language to view report

Download PDF